(ABNA24.com) A gobe Asabar ne aka shirya yin jana’izar shugaban mai rasuwa, inda ake sa ran halartar shuwagabannin da manyan jami’an kasashen duniya da dama a cewar fadar shugaban kasar.
Fadar shugaban kasar dai bata sanar da sunayen jami’an da zasu halarci jana’izar ba, saidai wasu kafofin yada labarai sun ce shugaban kasar faransa Emanuel Macon na daga cikin wadanda zasu halarci jana’aizar a gobe Asabar.
Mirigayi Beji Caïd Essebsi, shi ne wani shugaban kasar Tunisia, na farko da aka zabi bisa tsarin demokuradiyya a shekara 2014, bayan guguwar neman sauyi data yi awan gaba da tsohon shugaban kasar na waccen lokacin Ben Ali.
Ya rasu a jiya Alhamis yana mai shekaru 92 a duniya.
Jaridun kasar da dama sun martaba mutumin, ta hanyar buga labarai a rubutu baki da fari.
/129
27 Yuli 2019 - 06:28
Lambar labari: 964692
A Tunisia, ana ci gaba da nuna alhini, boyo bayan rasuwar shugaban kasar Beji Caïd Essebsi, wanda Allah,ya yi wa rasuwa jiya Alhamis.